Showing posts with label wheat.. Show all posts
Showing posts with label wheat.. Show all posts

Tuesday, 28 January 2020

funkasau da miyar lawashi

Funkasau da miyar lawashi.
Funkasau:
1.alkama
2.alabasa
3.yeast
4.gishiri
5.sugar
Miyar lawashi:
1.lawashi
2.tattasai
3.attarugu
4.albasa
5.maggi da onga
6.gyada
7.nama/kifi

Yadda za'a hadasu:
Kisamu alkamarki ki gyarata a surfa a regeta sai a kaita nika. Idan tadawo daga nika saiki tankade ki saka mata dan gishiri da sugar, ki yanka albasa kanana kanana ki zuba yeast dinki saiki kwaba da ruwan dumi kamar kwabin pop pop . Idan ya kumbura saiki daukoshi ki sanya manki mai yawa a kasko. Kada kicika masa wut ki barshi tsaka tsaki. Saikina debo kullin kamar na cin cin din pop pop saikina saka babban yatsanki a tsakiya kina hudawa kamar donut sannan ki sakashi a mai. Idan ya soyu ki juya daya gefen. Note: bayason wuta sosai kibarshi ya soyu a hankali dan alkamar ta nuna.
Miyan lawashi: 
Kiyanka lawashinki, idan kinaso da dan alaiyhu. Saiki jjjaga kayan miyanki ko ki markada. Ki sulala namanki da gishiri da albasa. Saiki nika gyadanki. Ki soya kayanmiyar tareda gyadar miyar, idan sun soyu saiki kawo ruwanki dan kadan kisaka dan lawashi bayason wuta. Idan kayanmiyan da gyadar sun nuna tareda maggi da ongan ki, saiki kawo sulalenki da kifinki kisaka tareda ganyen ki juya. Kirufesu na minti uku zuwa biyar shikenan miyar lawashinki tayi sai chi!