Kayan hadi:
Wake gwan gwani 2
Attarugu da albasa (dai dai yadda kakeso)
Gishiri (dai dai dandano)
Mangyada rabin kwalba
Yadda akeyi
1.Dafarko za'a surfa waken a fidda hancinsa (bawonsa). Sai a wanke arege idan akwai kasa aciki zai fita. Sai a tsane waken dan ba'ason ya jika. 2.Azuba tarugu da albasan a markadasu tare.
3.Idan aka markado sai a zuba masa gishiri a buga sosai, idan yayi kauri sosai sai akara ruwa yayi dai dai kada yayi ruwa sosai.
4.Sai a saka mai a wuta yayi zafi, sai a fara diban kullin ana soyawa.
Note:
Ba'a son waken kosai ya jika bayan an wanke baya gardi da kyau.
Sirrin kosai mai kyau shine buga waken nan har saiya kara auki yayi sakwalan ma'ana yadawo ba nauyi kaman kumfa, zakiga kinazubashi a mai zai taso. Amma idan kosai ya kwanta a mai toh bai buguba kokuma yayi ruwa sosai.