kayan hadi:
*flour
*tarugu da albasa
*maggi/gishiri
*manja ko mangyada
idan kika tanadi wadannan kayan hadi. saiki markada ko jajjaga kayan miyan ki, kisaka akwano. kikawo flour kizuba, kisaka maggi da gishiri idan kinada bukata, sai kizuba ruwa dai dai misali kwabin kamar kullin alale. sai ana diba ana soyawa a kasko da manja dan dai dai, idan gefe daya ya soyu sai a juya daya gefen. ana saka manja adan gefe da gefen dan karya kama.
Alura kada acika masa wuta, abarshi ya nuna a hankali, kafin ajuya inba hakaba zaiyi ruwa ruwa maimakon ya tsane ya kuma soyu.