Thursday, 15 July 2021

Awara

Kayan hadi
Waken suya
Tsamiya/ruwan tsari/ruwan kal
Tarugu da albasa(gamaiso) 
Gishiri (ga maiso)
Kwai (ga maiso) 
Mangyada
Yadda akeyi
Da farko za's taince waken suya, a wankeshi, Sai a markadashi.
Bayan an markada, sai a taceshi da abun tata mai laushi sosai. Sai a dorashi a kan wuta. Idan ya kusa tafasowa sai a tanadi ruwan tsari, tsamiya ko ruwankala kusa. Yana fara tafasowa kafin kumfar ta zubo sai aa zuba kashi daya bisa uku na ruwan. Idan ya sake tasowa akara zuba wani kashin har sai yadaina kumfar kokuma ruwan kullin yadawo mai haske kamar ruwa ma'ana duk awarar ta dinkule basauran kulli. Sai akwashe awarar a matsami ko abun tata a matse ruwan, awannan lokaci za'a zuba jajjagen tarugu daalbasa ga maisonshi sai amatsesu tare. Abarshi kamman minti shabiyar yayi dan karfi kadan yakuma chure wajeguda. Za ayankashi yadda akeso. A dora kaskon suya azuba mai aciki yayi zafi. Ga masu son gishiri sai a jika gishirin ana tsoma awarar a ruwan Sannan a soya. Idan da kwaine sai a fasa kwan asaka gishirin aciki a soya.

Alura:
Ba'a jika waken suya, kawai gyarata akeyi a wanke.
 Akwai kumfa da awara takeyi, idan ba'aso sai a diga manja kadan akullin kafin atache.

KOSAI

Kosai dai abincine na hausawa wanda kowa tashi yayi yaganshi.
Kayan hadi:
Wake gwan gwani 2
Attarugu da albasa (dai dai yadda kakeso)
Gishiri (dai dai dandano)
Mangyada rabin kwalba
Yadda akeyi
1.Dafarko za'a surfa waken a fidda hancinsa (bawonsa). Sai a wanke arege idan akwai kasa aciki zai fita. Sai a tsane waken dan ba'ason ya jika. 2.Azuba tarugu da albasan a markadasu tare.
3.Idan aka markado sai a zuba masa gishiri a buga sosai, idan yayi kauri sosai sai akara ruwa yayi dai dai kada yayi ruwa sosai. 
4.Sai a saka mai a wuta yayi zafi, sai a fara diban kullin ana soyawa.
Note:
Ba'a son waken kosai ya jika bayan an wanke baya gardi da kyau.
Sirrin kosai mai kyau shine buga waken nan har saiya kara auki yayi sakwalan ma'ana yadawo ba nauyi kaman kumfa, zakiga kinazubashi a mai zai taso. Amma idan  kosai ya kwanta a mai toh bai buguba kokuma yayi ruwa sosai.