Thursday, 30 January 2020

Yam balls

Kayan hadi:
1. doya
2.albasa
3.maggi
4.tattasai
5.attarugu
6.tumatur
7.kwai
8.mangyada

Ki fere doyarki ki yayyanka ta, ki wanke kisata a tukunya da ruwa dan kadan, sai ki zuba dan maggi a ciki. Idan ta tsane saiki gurza albasarki ko ki jajjaga tayi lumui, sai kirba doyrki da albasar, ki kwasheta a ajiyeta daban. Daga nana saiki samu tumatur mai kyau ki chopping dinta mitsi mitsi, da albasa, da tarugu. Kisanyasu a kasko ki soya da kayan hadinki, kiyi yar sauce da ita. Saiki dauko kirbabben doyanki kina gutsura ki mulmula sannan saiki matseta a tafin Hannunki kamar daddawa saiki debo sauce dinnan kina zubawa a tsakiyar sannan saiki nade ki rufe hadin ki mulmuleta kamar kwallo. Saikiyi tayi har sai hadin ya kare. Saiki fasa kwanki da kika yankawa albasa kika sakawa gishiri ko maggi, sikina tsomawa a ciki kina soyashi a cikin mai, idan ya soyu sai a kwashe a ci.  

Note : sauce din da kauri zakiyi kada yayi ruwa inbahaka ba zai hana ball din yayi kyau.

Wednesday, 29 January 2020

lettuce salad

I dan kika samu ganyen lettuce da tumatur,albasa,lawashi,tattasai,mangyada da garin karago, saiki jerasu haka ki tsiyy mangydnki akai saiki ajiye karagon sai anzo ci ki barbada( idan kinada kwai ki dafa ayayyanka akai)😋. Dadinsa yaban mamaki sosai saikun gwada zaku bani labari.

Amfanin turmeric(kurkur)

Amfanin turmeric a girki yanada yawa. na farko basai kin cika curry a girki ba. zaki saka kadan kamshint ya isheki. saiki sany turmeric dinki it kuma zat sanya miki wannan yellow kalan. idanma kinaso tayi kamar green dinnan saiki saka curry dinki da dan yawa kisa turmeric zasu baki kala g nashi kamshin shima. gashi yana gyra fata yana magun guna da yawa g dankaren araha da yake dashi. Danyrta tana kama da citta. duk wacce ta gwada zata bani labari, karku manta snapping min pic na girkin.

Tuesday, 28 January 2020

funkasau da miyar lawashi

Funkasau da miyar lawashi.
Funkasau:
1.alkama
2.alabasa
3.yeast
4.gishiri
5.sugar
Miyar lawashi:
1.lawashi
2.tattasai
3.attarugu
4.albasa
5.maggi da onga
6.gyada
7.nama/kifi

Yadda za'a hadasu:
Kisamu alkamarki ki gyarata a surfa a regeta sai a kaita nika. Idan tadawo daga nika saiki tankade ki saka mata dan gishiri da sugar, ki yanka albasa kanana kanana ki zuba yeast dinki saiki kwaba da ruwan dumi kamar kwabin pop pop . Idan ya kumbura saiki daukoshi ki sanya manki mai yawa a kasko. Kada kicika masa wut ki barshi tsaka tsaki. Saikina debo kullin kamar na cin cin din pop pop saikina saka babban yatsanki a tsakiya kina hudawa kamar donut sannan ki sakashi a mai. Idan ya soyu ki juya daya gefen. Note: bayason wuta sosai kibarshi ya soyu a hankali dan alkamar ta nuna.
Miyan lawashi: 
Kiyanka lawashinki, idan kinaso da dan alaiyhu. Saiki jjjaga kayan miyanki ko ki markada. Ki sulala namanki da gishiri da albasa. Saiki nika gyadanki. Ki soya kayanmiyar tareda gyadar miyar, idan sun soyu saiki kawo ruwanki dan kadan kisaka dan lawashi bayason wuta. Idan kayanmiyan da gyadar sun nuna tareda maggi da ongan ki, saiki kawo sulalenki da kifinki kisaka tareda ganyen ki juya. Kirufesu na minti uku zuwa biyar shikenan miyar lawashinki tayi sai chi!